Amazon zai yi aiki da jirgi mara matuki

Hakkin mallakar hoto Amazon
Image caption Jirgin mara matuki zai dauki kunshin kaya mai nauyin kilogram 2.3

Kamfanin Amazon mai sayar da kayayyaki ta intanet ya bukaci kwararru masu tafiyar da kananan jirage marasa matuka da su ba shi hayar jiragen ya rika aikawa da kayayyaki.

Kamfanin zai rika amfani da tsarin Prime Air wajen aikawa da kunshi kunshin kayayyaki masu nauyin kilogram 2.3 ta kananan jiragen ga wadanda suka saya ta intanet a cikin mintoci 30.

Za a yi gwajin aikawa da sakonnin ta jiragen marasa matuka a wani wurin da Amazon ya mallaka a Cambridge bayan ya saye fasahohin Evi.

A cikin watan Disamban 2013 ne kamfanin Amazon ya sanar da shirin sa na kirkiro tsarin aikawa da sakonni ta Prime Air, kuma ya ce za a iya kwashe shekaru biyar kafin a fara aiki da tsarin gadan-gadan.

Sauran kamfanoni da suke amfani da jirage marasa matuka wajen aikawa da sakonni sun hada da Google, da DHL.

A lokacin bazara, kamfanin Google ya bayyana yin amfani da kananan jiragen, sannan a watan Satumba, kamfanin DHL ya fara aikawa da sakonni gadan-gadan ta kananan jirage marasa matuka zuwa wani tsibiri a tekun arewacin turai.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amazon zai rika amfani da jiragen marasa matuka ne domin bunkasa kasuwancinsa

A cikin wannan makon ma, kwalejin bincike ta Imperial da ke Burtaniya ta ce ta na kashe fam miliyan daya da dubu dari biyu da hamsim wajen samar da dakin gwaji don bunkasa kwarewar Burtaniya a fannin jirage marasa matuka.

A cikin shekarar 2016 ne za a kammala aikin ginin dakin gwajin, wanda zai kasance da babbar haraba a rufe.

Hukumomin kula da sararin samaniya a kasashen Burtaniyta da Amurka sun takaita wuraren da kananan jirage marasa matuka za suyi zirga zirga.

A Burtaniya, wajibi ne masu sarrafa jiragen marasa matuka su nemi izini, sannan ba a yarda jiragen su yi shawagi a inda akwai taron mutane da yawansu ya kai 1000, ko kuma a tsakanin gidaje miliyan 50.

A Amurka ma dole masu sarrafa jiragen su nemi izini.