Bam ya kashe akalla mutane 13 a Azare

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga garin Azare a jihar Bauchi a Nijeriya na cewa akalla mutane goma sha uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu kimanin hamsin suka jikkata a wani harin bam a wata kasuwa.

Ganau sun ce wata 'yar kunar-bakin-waken ce ta ta da bam din a wata kasuwar sai da kayan wayoyin salula.

Kazalika bayan tashin bam din matasan garin sun bazama kan titi suna zanga-zanga, suna Allah wadai da 'yan siyasa, inda suka kona hotunan 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban, masu mulki da 'yan adawa sabo da suna zargin cewa matsalar tsaron da ake fuskanta na da nasaba da halayyar 'yan siyasar.

Wannan shi ne karo na biyu da ake samun harin kunar-bakin-wake a garin na Azare a cikin wata guda.