Boko Haram ta kwace iko da garin Chibok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Watanni bakwai kenan da sace 'yan matan Chibok

Bayanai daga jihar Borno sun nuna cewar 'yan kungiyar Boko Haram sun kwace Chibok, garin da suka sace 'yan mata dalibai a wannan shekarar.

Rahotanni sun nuna cewar 'yan Boko Haram din sun kaddamar da hari ne a garin a yammacin ranar Alhamis.

Wasu mazauna garin Chibok sun ce sojojin da ke garin sun arce a lokacin da 'yan Boko Haram suka shigo garin.

Sanata Muhammed Ali Ndume da ke wakiltar kudancin Borno a majalisar dattijan Nigeria ya shaidawa BBC cewa 'yan Boko Haram kimanin 400 sun shiga garin Askira Uba, kana suka nufi garin na Chibok da ke da makwabtaka da Uba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen 'yan matan sun shiga cikin damuwa

A watan Afrilu ne 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 daga garin na Chibok, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Batun dai ya janyo wa shugaban Goodluck Jonathan kakkausar suka inda suke zargin gwamnati da jan kafa wajen ceto 'yan matan.

A nata bangaren, gwamantin kasar ta ce tana yin bakin kokarinta wajen kubutar da 'yan matan.