'Yan Boko Haram sun sake kai hari a Chibok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan Afirilu ne dai 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 daga garin na Chibok, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Rahotanni daga Nigeria na cewa wasu da ake zargi 'yan Boko Haram sun sake kai hari a garin Chibok na jihar Borno.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewa wannan lamari dai ya auku ne a ranar Alhamis.

Da ma dai wani dan majalisar da ke wakiltar yankin ya shaidawa BBC cewa 'yan Boko Haram kimanin 400 sun shiga garin Askira Uba, kana suka nufi garin na Chibok da ke da makwabtaka da Uba.

Jami'an tsaro dai ba su kai ga tabbatar da labarin ba.

A watan Afirilu ne dai 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 daga garin na Chibok, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Batun dai ya janyo wa shugaban kasar bakin jini har ma wasu na ganin bai mayar da hankali wajen ceto 'yan matan ba.

A nata bangaren, gwamantin kasar ta ce tana yin bakin kokarinta wajen kubutar da 'yan matan.

Karin bayani