An kai hari a Gombi da Hong da Askira Uba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rahotannin sun ce an kai hare-haren ne a Gombi da Hong da kuma Askira Uba

Rahotannin da muka samu daga garin Gombi na jihar ta Adamawa na cewa, wasu da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram din ne, sun shafe daren Alhamis da safiyar Juma'a suna ta harbe-harbe a cikin garin.

Mazauna garin sun shida wa BBC cewa, mutane da dama sun fice daga garin da maraicen Alhamis tun lokacin da suka samu labarin 'yan Boko Haram din sun shiga garin Hong da ke makwabtaka da Gombin.

Kazalika, mazauna garin Askira Uba da ke jihar Borno sun ce 'yan Boko Haram sun kai musu hari a ranar ta Alhamis da daddare.

Dan majalisar wakilai Hon Peter Biye ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko haram -- kimanin 400 -- sun je garin ne a kan babura da motoci kuma sun yi barna da yawa.

A cewarsa, 'yan Boko Haram din sun nufi garin Chibok da ke kusa da Askira Uba, amma 'yan banga sun fito wajen garin domin hana su shiga.

Babu dai karin bayani game da halin da ake ciki yanzu a garin na Chibok.

Karin bayani