Babbar badakala a kamfanin mai na Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matsalar cin hanci a kamfanin Petrobas ta fi fitowa lokacin zaben watan jiya

'Yan sanda a kasar Brazil sun gudanar da jerin samame tare da cafke mutane 18 a wani binciken badakalar cin hanci da rashawa a babban kamfanin mai na kasar Petrobas.

Jami'an 'yan sanda sama da 300 ne suka binciki wasu manyan kamfanoni a wasu jihohi biyar a game da badakalar cin hancin da rashawa.

Tsohon shugaban kamfanin, Paulo Roberto Costa wanda aka kame a cikin watan Maris, ya ce matatar mai ta kasar ta na tafiyar da wani asusu da ake karkatar da kudi zuwa hannun jam'iyyun siyasa, ciki harda jam'iyar ma'aikata ta shugabar kasar Dilma Roussef.

'Yan sanda sun ce sun kame wasu kadarori na kimanin dala miliyan 270 mallakin mutane 36.