"Buhari" ya yi wa Buba Galadima raddi

Image caption Magoya bayan Buhari sun ce zai sake yin takara ne saboda ci gaban Nigeria

Wasu mutane da ke goyon bayan Janar Muhammadu Buhari a Nigeria sun ce bukatar ci gaban kasar ce ta sa ya sake fitowa neman shugabancin kasar a 2015.

Daya daga cikin mai goyon bayan Janar Buhari, Faruk Aliyu, ya bayyana hakan ne bayan wani jigo a jam'iyyarsu ta APC, Injiniya Buba Galadima ya ce ba zai goyi bayan Buhari a zaben 2015 ba saboda a baya, Buharin ya yi alkawarin ba zai sake yin takara ba.

Faruk ya ce kalaman Buba Galadima sun ba su mamaki, yana mai cewa "nunkufurci" ne ya sa Buba ya daina goyon bayan Janar Buhari.

Masu fashin-bakin siyasar Nigeria dai na ganin cewa hakan na nuna cewa an samu baraka tsakanin Janar Buhari da mutane da a baya aka sansu da goyon bayansa.

Karin bayani