Jirgin soji ya sake faduwa a Adamawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan ne karo na biyu jirgi na yin hadari a jihar a cikin mako daya

Wani jirgin sama da ake zaton yana dauke da makamai ya yi hadari a garin Girei na jihar Adamawa da ke arewacin Nigeria a daren Alhamis.

Hadarin jirgin ya zo ne kwanaki uku bayan wani jirgin sojojin kasar ya rikito lokacin da yake shawagi a wani kauye a yankin karamar hukumar ta Girei.

Babu tabbacin wurin da jirgin ya nufa kafin hadarin a daren na Alhamis, kuma wasu abubuwa sun yi ta fashewa lokacin da jirgin ke ci da wuta.

Wasu mazauna garin Girei sun shaidawa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu jirage biyu ke kokarin wucewa ta garin zuwa inda jami'an tsaron kasar ke yaki da 'yan kungiyar Boko Haram a jihar.

Karin bayani