Za a jinkirta kuri'a kan 'yancin Internet

Shafin Internet Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shafin Internet

Hukumar Sadarwa ta Tarayya za ta jinkirta kuri'a a kan 'yancin Internet.

An ba da rahoton cewa, hukumar dake sa ido kan harkokin sadarwa ta Amurka da ake kira FCC a takaice, za ta jinkirta wata shawara a kan yadda za ta sa ido kan hanyar sadarwa ta Internet har ya zuwa shekara ta 2015.

A 'yan kwanakin nan muhawara ta karu dangane da bayar da matsayi daya kan 'yancin hanyar sadarwar ta internet.

Shugaba Obama ya fada a wannan makon cewar yana so hukumar kula da harkokin sadarwar ta Tarayya ta gitta dokoki masu karfi don kare matsayin 'yan ba-ruwanmu na internet.

Hukumomin dake hada mutane da hanyar sadarwa ta Internet sun ce za su yaki duk wani yunkuri na kafa dokoki masu tsauri.

Sakataren watsa labarai ta hukumar mai sa ido kan hankokin sadarwar ta Amurka Kim Hart ya tabbatar ma BBC cewar, za a jinkirta yanke shawara kan batun har sai zuwa shekara mai zuwa.

Yace, "ba za a kada kuri'a ba a kan internet a cikin watan Disamba kamar yadda aka shirya". Wannan na nufin a yanzu za a kammala dokokin ne a shekara ta 2015.

Tun farko, hukumar ta FCC ta ce, zuwa karshen wannan shekarar za ta yanke shawara.

Muhawarar, ta maida hankali ne kan ko yakamata a bar kamfanoni masu tafiyar da hanyoyin sadanrwa na internet su caji wasu kamfanonin sadarwa. Don karfafa yadda ake samun layukkan su.

Hukumomin sadarwar na internet sun yi tankiya cewar kamata ya yi a kyale su, su caji karin kudi saboda masu aikewa da bayanai masu nauyi, to amma masu da'awar kare 'yancin masu mu'amalla da hanyar sadarwar ta internet sun ce, yin hakan zai tauye akidar bayar da 'yancin amfani da internet bai-daya ga kowa.

Kamfanonin sadarwa ta internet da dama sun yi turus lokacinda Shugaba Obama ya ba da sanarwa yana kira ga hukumar kula da harkokin sadarwar ta tarayya ta kassafa su, ta yadda za a gitta musu dokoki kamar sauran kamfanoni.

Karin bayani