Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalolin raba katin zabe

Hukumar zaben Najeriya INEC na aikin raba katin zaben din-din-din wanda da shi ne za a yi babban zaben kasar na badi.

A watan Fabrairu mai zuwa ne aka tsara za a gudanar da babban zaben.

Sai dai aikin rajistar ya gamu da matsaloli a wasu sassan Najeriyar.

Matsalolin dai sun sa wasu na sukar lamarin hukumar zaben da kuma nuna shakku a kan ko INEC din za ta iya gudanar da sahihin zabe a kasar a badi ko kuma a'a.