Amurka: Ana yin galaba a kan kungiyar IS

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Hagel ya ce ya dole ne a shirya daukan lokaci mai tsawo a na wannan gwagwarmaya

Manyan jami'an ma'aikatar tsaron Amurka sun ce a na samun nasara a matakin soji da a ka shafe watanni uku ana dauka akan mayakan kungiyar IS.

Sai dai sunyi gargadin cewa gwagwarmayar da Amurka da kawayenta da ke cikin hadakar dake yaki da kungiyar keyi, ba mai sauki bace.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel da babban hafsan hafsoshin kasar, Janar Jack Dempsey ne suka sanar da hakan lokacin da suka bayyana a gaban 'yan majalisar dokokin kasar.

Mista Chuck Hagel ya ce hadakar dakarun da Amurka ke jagoranta, ta yi nasarar hana mayakan kungiyar IS cigaba da dannawa, duk da cewa a wasu lokutan suna nuna gagara a wasu yankuna a Iraki da Syria.