An daure King akan cin zarafi a WhatApp

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Buduruwar Luke King ta ce ita ta aika mushi hotunan tsaraicinta don ya gani shi kadai

An daure wani mutun a gidan kurkuku a Burtaniya saboda ya yada hoton tsaraicin tsohuwar buduruwarsa ta dandalin sada zumunci na WhatApp.

Luke King wanda a baya ya yi barazanar sanya hotunan tsaraicin matar a intanet, ya sauya hoton shafinsa na WhatApp da daya daga cikin hotunan matar.

Matar wadda ta fito daga Derbyshire, ta shaida wa 'yan sanda cewa ta yi bakin ciki da yada hotunan tsaraicin nata.

An yanke wa Luke King wanda ke zama a Nottingham daurin makonni 12 a gidan yari sakamakon laifin da ya aikata.

Wata kotun Majistire a Derbyshire ta Arewa ta yanke wa Luke King hukunci, inda ya amsa ya aikata laifin a ranar 8 ga watan Agusta.

Buduruwar tasa ta shaida wa 'yan sanda cewa ita ta aikewa saurayin nata hotunan tsaraicin nata domin ya gani shi kadai.

'yan sandan suka ce a baya matar ta kai musu koke lokacin saurayin nata ya fara barazanar yada hotunan a intanet, amma 'yan sanda suka gargade shi.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce ''yana da kyau mutane su fahimci cewa laifi ne su ci zarafin wasu ta irin wannan hanya. Mun yarda da hukuncin alkali cewa wannan ba abune mai kyau ba, musanman bayan an gargadi Luke King akan yin hakan''.

An yanke wa King hukuncin daurin makonni 12 ne bisa amfani da dokar kare mutane daga cin zarafi ta 1997.

Amma a karkashin sabuwar dokar, wadanda a ka samu da laifin yada hotuna ko bidiyon tsaraicin wani ko wata za su fuskanci daurin shekaru 2 a gidan yari.