'Hankali ya fara kwanciya' a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano dake arewacin Najeriya tace hankali ya fara kwanciya bayan fashewar wani bam a jiya.

Wani kakakin 'yan sandan ya shaidawa BBC cewa sun tsaurara matakan tsaro a jihar, bayan lamarin na jiya da yayi sanadiyar mutuwar mutane 6.

Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar, wadda ta faru a kusa da wani gidan mai na NNPC lokacin da wata motar dakon mai ke sauke kaya.

Bayanai sun nuna cewa wurin da aka samu fashewar, matattarar jami'an tsaro ce, sannan kuma mutane na gudanar da hada hada a wajen.

Wata dake unguwar Hotoro, inda bam din ya fashe da shaidawa BBC cewa har yanzu suna cikin "fargaba da tashin hankali."

Babu wani ko wata kungiya data dauki al'hakin kai harin, amma a baya, kungiyar Boko Haram ta sha kai irin wannan hari a jihar.

Karin bayani