Taron G20: An ja kunnen Rasha

Hakkin mallakar hoto EPA

Shugabannin kasashen yamma da suka hallara a Australia saboda taron G-20 sun gargadi Rasha da ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta, ko ta fuskanci karin takunkumi.

Firai Ministan Burtaniya, David Cameron, ya fadawa Shugaba Putin cewa dangatar Rasha da sauran kasashen Turai za ta yi muni idan har dakarun Kremlin suka ci gaba da zama a Ukraine.

Shugaba Obama ya bayyana matakin da Rasha ke dauka a Ukraine a matsayin wani abu mai ban tsoro.

Mr Putin wanda rahotanni ke cewa yana shirin barin taron kafin a kammala shi ya ce takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakabawa kasarsa basu halarta ba.