Ana leken wayoyin mutane ta jirgi a Amurka

Leken sirrin wayoyin salula ta jirgi Hakkin mallakar hoto CFP
Image caption Leken sirrin wayoyin salula ta jirgi

A cewar Mujallar Wall Street, jirage na gwamnati Amurka tana shawagi a sararin samaniya da na'urorin dake tattara bayanai na miliyoyin wayoyin salula.

Rahoton ya yi ikirarin cewa, na'urar tana tattaro bayanai ne daga hasumiyai kamfanonin wayoyin salula da wayoyin salular dake hannun mutane a wuraren da suke.

A yayinda ake amfani da su don bin sawun wasu mutane da ake zargi, dukkan wasu na'urori na wayoyin salula dake yankin da aka ratsa da ita za su samu signa na nau'urar.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka dai ta ki tabbatarwa ko kuma musanta wannan rahoto.

Mujallar Wall Street ta ce ta tuntubi majiyoyi da suke da masaniya game da wannan shiri wadanda suka ce Jirgin saman Cessna wanda aka lika ma na'urorin suna shawagi daga akalla filayen jiragen sama biyar na Amurka.

Sashen dake wannan aiki ya ce yana aikin ne a farfajiyar doka ta tarayya.

Naurar da jirgin ke shawagi da ita tana kwaikwayon irin signa ne na kamfanonin wayoyin salula wanda ke sanya wayoyin mutane karbar wannan signa, kuma idan sun yi haka sai su tura bayanai na rajistar masu wayoyin da ma wurinda suke a lokacin.

A yayinda ake amfani da su musamman don bin sawun wani mutum ko wata karamar kungiya ta wasu mutane, dukkan wayoyin dake wannan yanki, za a kwashi bayanansu a wannan leke na asiri.

Wani kwararre kan sha'anin tsaro Farfesa Alan Woodward ya gaya ma BBC cewa suna aiki ne kamar yadda wata na'ura ta musamman mai bin sawun wayoyi ke aiki.

Yace, "gwamnati tana da kafar samun wannan na'ura, don sa ido kan wayoyin salula, to amma ba gwamnati kadai ba, kowa ma yana iya sayen na'urar a kan kudi fam dubu biyu, ga wanda ke so shi ma ya kafa kamfaninsa na leken asirin wayoyin salula na mutane.

Karin bayani