Garin Chibok ya koma hannun sojojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya sojojin kasar sun yi ikirarin cewa sojoji sun sake kwace garin Chibok daga hannun 'ya'yan kungiyar nan ta Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Nigeria Brigadier General Olajide Olaleye shi ne ya tabbatarwa da BBC wannan labari.

A ranar Alhamis ne kungiyar Boko Haram ta kwace garin Chibok bayan fafatawa da Sojojin Nigeriar.

Chibok shi ne garin garin da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan matan sakandare fiye da 200.