Nigeria za ta tsuke bakin aljihu

Image caption Ministar kudin Nigeria ta ce za su tashi tsaye wajen samun kudade ta wasu fannoni

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki matakan tsuke-bakin-aljihu, saboda gibin da ta samu a kudaden shigarta saboda faduwar farashin mai a duniya.

Gwamnatin ta ce za ta aike wa majalisar dokokin kasar bukatar zaftare kasafin kudin kasar daga trillion 4 da biliyan 800 zuwa trillion 4 da biliyan dari shida da sittin.

Ministan kudin kasar Farfesa Ngozi Okonjo Iweala ta ce za a sakko da kiyasin da aka yi amfani da shi wajen tsara kasafin kudin daga dala 78 kan gangar mai zuwa 73

Farashin danyen mai dai ya yi faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru hudu daga dala 118 a kan kowace ganga zuwa dala 79.

Matakan da gwamnati za ta dauka sun hada da takaita tafiye-tafiyen jami'anta zuwa kasashen waje a shekara mai zuwa.

Za ta kuma kara haraji kan kayan alfarma da ake shigo da su kasar, kamar manyan motoci da jirage da giyar champagne.

Gwamnatin za ta dakatar da sayen sabbin na'urori sai abin da ya zama dole, sannan za ta duba batun hukumomin da ayyukansu suka zama kusan daya.