An rufe taron kasashen G20

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Batun rikicin Kasar Rasha da Ukraine ya taso a taron G20

An kammala taron kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a duniya da cikakken jawabi a kan irin yarjejeniyoyin da suka cimma, wadanda suka shafi habbaka tattalin arziki.

Firayim Ministan Australia, Tony Abbott ne ya gabatar da jawabin, wanda ya ce idan aka cika alkawuran da aka dauka, to tattalin arzikin duniya zai habaka, tare da samar da miliyoyin ayyukan yi nan da shekaru biyar masu zuwa.

Taron ya kuma caccaki Firai Ministan Rasha sabuda rawar da kasarsa take takawa a Ukraine.