Batun jihadi a Internet ya damu Barittaniya

Yara 'yan jihadi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yara 'yan jihadi

Fadar gwamnatin Brittaniya Downing Street na kara matsin lamba kan kamfanonin sadarwa na internet su bullo da wani tsari da zai rinka nuna akidoji na jihadi da ake yadawa ta internet.

Fadar ta Downing Street tace, Manyan kamfanonin dake hada jama'a da internet a Brittaniyar za su bullo da sabbin matakai na magance yadda a kan cusa ma mutane tsattsauran ra'ayin addini ta Internet.

Kamfanonin sadarwar na Internet sun kuduri aniyar kara karfin na'urorin dake ta ce bayanai da kuma kara wani malatsi da zai rinka nuna bayanai na wasu al'amurra na ta'addanci.

To amma kamfanonin sadarwar na Internet sun gaya ma BBC cewar babu wata yarjejeniya takamaimai da aka kulla da su kan wannan batu.

Masu fafutuka sun yi kiran da a rinka nuna abinda za a toshe a shafin na internet.

Prime Minista David Cameron ya ce kamfanonin na fasaha suna da wani alhaki da ya rataya ga wuyansu na kawar da akidojin da masu jihadin ke yadawa ta Internet.

Mr Cameron ya sheida ma Majalisar dokokin Australia a Canberra cewar yana matsa lamba a kan kamfanonin fasaha su rinka toshe bayanai da rubuce-rubuce na masu jihadi a shafukkan su.

Yace, "a Brittaniya muna matsa musu lamba su kara daukar matakai abinda ya hada da karfafa nau'rar dake tace bayanai, su kuma kara tashi tsaye wajen kawar da irin wadannan bayanai masu hadari."

Farfagandar da 'yan ta'adda ke yi ta watsu a kafofin sadarwa na Internet kamar a Twitter da Yutube.

"yace, muna samun cigaba, amma akwai sauran jan aiki a gaba. Wannan alhaki ne da ya rataya ga wuyan su - don haka muna neman su ma su yi aikinsu yadda yakamata.

Matakan da ake shawarar dauka an yi imanin sun taso ne daga wani taro da aka yi cikin watan jiya don tattauna hanyoyin da kamfanonin sadarwa za su iya taimakawa wajen magance yada akidoji na tsaurin ra'ayi ta Internet.

Karin bayani