Fashi na karuwa a tekun Afrika

Wasu matuka jirgin ruwa da 'yan fashi suka yi garkuwa da su Hakkin mallakar hoto mphrp.org
Image caption Wasu matuka jirgin ruwa da 'yan fashi suka yi garkuwa da su

Zai zo wa mutane da yawa da mamaki - idan suka ji cewa Somalia ba ta cikin sahun kasashen da a yanzu harkokin fashi akan ruwa ke haifar da barazana.

Wannan batu ba za a kira shi kamar wasannin nan da ake shiryawa a Hollywood ko daga abubuwa masu ban al'ajabi ba.

To amma batun fashi a sassan nahiyar ya kere na Somalia ta hanyoyin kai hare-hare a gabar teku.

Matsalar ta fara ne daga Nijeriya, inda mafi yawa akan samu fashin danyen man fetur a gabar tekun kasar. A yanzu sana'ar fashin a teku na ci kamar wutar daji, daga arewaci zuwa kudanci.

Na baya -baya shine na kwace wani jirgi a gabar tekun Angola dake a kudancin Africa.

Wakiliyar BBC Mary Harper ta duba mana wannan matsala ta fashi a teku a ziyarar da ta kai Nijeriya

Karin bayani