Gwamnatin Nigeria ba ta daukar shawara - Atiku

Image caption Atiku ya ce ya kamata a shigar da 'yan kato-da-gora aikin soja

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ba ta daukar shawara shi ya sa kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce hakan ne ya sa shi da tsohon mai gidansa, Cif Olusegun Obasanjo suka hada gwiwa kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro a kasar.

A cewarsa, sau da dama yana bai wa gwamanti shawarwari kan yadda za ta magance hare-haren 'yan Boko Haram amma ba ta dauki shawarwarin ba.

Alhaji Atiku ya ce, "Na taba ba da shawara a dauki kungiyoyin tsaro, watau Civilian JTF cewa a dauke su ayyukan soja, domin su suka fi kowa sanin 'yan Boko Haram, amma an ki yi.".

Kazalika, Atiku Abubakar ya ce: "Na biyu kuma shi ne tun da gwamnati kadai ba za ta iya maganin matsalar ba, to ta bar jama'a ko garuruwa ko kuma kauyuka su kafa kungiyoyin tsaronsu don kare kansu."

Karin bayani