An nada shugaban rikon-kwarya a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Michel Kafando ba zai tsaya takarar shugaban kasar ba

Sojoji da shugabannin kungiyoyi fafaren hula sun zabi tsohon ministan wajen Burkina Faso, Michel Kafando, a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar.

Sun dauki wannan mataki ne bayan wata yarjejeniya da aka kulla ranar Lahadi, wacce ta zayyana yadda za a gudanar da zabe a cikin shekara guda.

Mr Kafando na cikin mutane hudu da aka ware sunayensu domin zabar daya daga cikinsu ya zama shugaban rikon kwaryar.

Sauran mutanen sun hada da 'yan jaridu guda biyu da malamin jami'a.

Babban aikin da zai fara yi a yanzu shi ne ya zabi Firayim Ministan da zai jagoranci gwamnati.

Za dai a hana Mr Kafando tsayawa takara a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

Karin bayani