Kamaru na fuskantar matsi daga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na jiran kota kwana

Dakarun Kamaru na gumurzu da mayakan Boko Haram a kan iyakokin kasar da Nigeria.

Dakarun Kamarun sun girke makamai domin kai hari a kan 'yan Boko Haram wadanda ke kokarin kafa daular Musulunci a kauyen da ke kan iyakar.

A yanzu dai jama'a sun kaurace wa kauyen Amchide saboda yadda 'yan Boko Haram ke tsananta kai hare-hare.

Image caption Mutane na cikin mawuyacin hali

Dubban mutane na yin kaura zuwa wasu garuruwan inda suke loda kayayyakinsu a cikin amalanke domin su tsira da ransu.

'Dakaru na musamman'

"Kullum sai jin karar harbe- harbe," in ji Kwamandan dakarun Kamaru.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Amchide ya kusa zama kufai

A cewarsa lamarin na da tayar da hankali shi yasa suke yin likimo.

Ya kara da cewa "'Yan Boko Haram na nan kamar aljanu suna sa ido a kan yadda muke aiki domin sannin matakin da za su dauka."

A yanzu haka dai Kamaru ta tura dakaru na musamman 1,000 wadanda aka horar da su a Amurka da Isra'ila zuwa kan iyakar kasar da Nigeria domin murkushe 'yan Boko Haram.