Ana ci gaba da batun nukiliyar Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana tattaunawa kan batun makamin nukiliyar Iran.

Manyan shugabannin kasashe 6 na duniya wato Amurka, da Burtaniya da Faransa, da Jamus, da Rasha da kuma China za su gana a yau Talata a Vienna, domin sake tattaunawa dan samar da matsaya kan shirin Nukiliya na Iran kafin cimma wa'adin da aka tsaida na 24 ga wanann wata saboda batun.

Shugabannin kasashen na son ganin Iran bata kera makamin kare dangi ba, ya yin da a koyaushe Tehran ke nanata cewa shirin ta na Nukiliya na zaman lafiya ne.

To amma duk da haka akwai banbance-banbance akan yadda shirin bunkasa sinadarin Uranium na Iran din zai kasance nan gaba, da kuma lokacin da za a sassauta ko cirewa Iran takunkumi.

Sai dai wakilin BBC yace ana bukatar karin lokaci domin cimma matsaya da sasantawa kan batun.