An gano makamai a wani Masallaci a Kenya

Image caption 'Yan sanda a kasar Kenya

'Yan sanda a Kenya sun ce sun gano gurneti gurneti da albarusai sakamakon wani samame a wasu masallatai biyu a birnin Mombasa na gabar teku.

'Yan sanda sun harbe mutum daya har lahira, a lokacin samamen na asubahi.

Haka kuma an kama wasu mutanen fiye da 250 a samamen wanda aka fadada zuwa gidajen dake zagayen wuraren.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Geoffrey Mayek, ya nemi hadin kan 'yan kasar wajen yaki da masu tayar da kayar baya.