'Mata sun fi kai harin kunar bakin wake'

'Yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana yawan kai hare-haren kunar bakin wake da mata ke jagoranta a arewacin Nigeria.

A Nigeria, 'yan kasar, musamman mata na nuna takaici kan yadda aka fi yin amfani da 'yan uwansu mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukan su a 'yan watannin nan a ire-iren wadannan hare-hare da mata ke kai wa.

Masana dai na ganin cewa ana yin amfani da matan ne domin ganin ba a cika tsaurara matakan bincike akan su ba, saboda girmama su da ake yi da dogaro da cewar ba sa son tarzoma.

Wasu mata dai sun bayyana takaicinsu da abon salon da kungiyar ta Boko Haram ta fito da shi, a cewar su bai kamata maza su shiga wanann mummunar dabi'a ba bare kuma mata da suka kasance masu tausayi da jin kai.

An yi ittifakin cewar ba a fara amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake ba har sai da aka yi watanni biyu da sace 'yan matan sakandaren Chibok, lamarin da wasu ke zargin cewa mai yiwuwa ana amfani da wadannan 'yan mata ne don kai hare-haren.