An sa dokar hana fita a jihar Nassarawa

Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Gwamnan Nassarawa Alhaji Umar Tanko Almakura

Gwamnatin jihar Nassarawa a arewacin Najeria ta sanya dokar hana fita a Lafia babban birnin jihar daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe saboda wani rikici na kabilanci.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Lamai, ya ce, wasu 'yan kauyen Alakiyo ne suka saci shanun fulani, su kuma fulanin suka zo kwatar dabbobinsu abin da ya fara tayar da rikicin, daga bisani wasu mutanen suka kawo hari lafiya sai matasa suka yi kokarin korar su.

Sabon rikicin wanda ke da nasaba da kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum daya.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne ranar Litinin a garin na Lafia bayan hatsaniya tsakanin fulanin da 'yan kabilar Eggon.

Wannan rikicin ya faru ne kasa da kwana guda bayan wani rikicin tsakanin Kabilun Fulani da kuma 'yan Ombatse a kauyen Alakiyo wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyar da jikkatar wasu da kuma kone wasu ababan hawa.