Iyalan Bob Marley sun yi kayan kwalliya na ganyen wiwi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Ya'yan Bob Marley mata Cedella da Karen

Iyalan marigayi Bob Marley, sun kaddamar da abin da suka bayyana kayayyakin kwalliya na farko a duniya na sanfurin ganyen wiwi.

Za a kira sanfurin kayayyakin Marley Natural, kuma za a yi amfani da samfurin wajen sayar da man shafawa da sauran kayan amfanin jama'a da aka yi da ganyen wiwi.

'Yar marigayi Bob Marley, Cedella, ta ce babanta zai yi farin ciki ya ga mutane suna fahimtar amfanin abin da ta bayyana tasirin ganyen wajen warkar da cututtuka.

Bob Marley ya mutu ne a 1981, kuma ya riki ganyen wiwi a matsayin wani fanni na addinisa na Rastafari.

Makadin Reggaen ya kuma goyi bayan dokar halatta amfani da ganyen.

Ana sa ran fara sayar da kayayyakin a Amurka kuma kila har a sauran kasashen duniya daga badi.