Boko Haram: Matasa sun kona wani a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hakan na zuwa kwanaki bayan kiran da Sarkin Kano ya bukaci mutane su kare kansu

Rahotanni daga jihar Gombe a Nigeria na cewa wasu matasa da suka fusata sun kona wani da ake zargi yana dauke da bama-bamai.

Dumbin matasan dai sun sanya wa mutumin taya kuma suka kona shi kurmus a wata tashar mota da ke birnin.

Wani wanda ya shaida lamarin ya gaya wa BBC cewa mutumin ya ki yarda a bincike shi kamar yadda ake binciken mutane a tashar, kuma daga bisani ya yarda jakarsa wadda ke dauke da bama-bamai.

Rundunar 'yan sandan jihar ba ta yi wani karin bayani game da lamarin ba, amma an killace manyan titunan kusa da wurin.