Boko Haram: An kashe sojoji 10 a Gombi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani mutum ya ce ya ji karar harbe-harbe da safiyar ranar Talata

Rahotanni daga garin Gombi na jihar Adamawa da ke Nigeria sun ce sojoji goma da 'yan Boko Haram da dama sun mutu bayan wani gurmuzu da bangarorin biyu suka yi.

Hakan dai na faruwa ne a lokacin da sojojin ke korarin kwace garin na Gombi, wanda ake yi masa kallo a matsayi wata kofa ta shiga Yola, babban birnin jihar.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ya ji karar harbe-harbe ranar Talata da safe, sai dai bai san ko hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane ba.

Ya kara da cewa 'yan Boko Haram sun fice daga garin kuma babu soji ko guda daya da aka girke domin tabbatar da tsaro.

'Yan Boko sun kama garin na Gombi ranar Alhamis da ta gabata, bayan an fatattake su daga Mubi.

Karin bayani