Falasdinawa sun kashe Yahudawa hudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An soma zaman dar dar a birnin Kudus

Wasu matasan Falasdinawa su biyu dauke da bindigogi da wukake, sun kashe mutane hudu a wajen wani idaba na Yahudawa dake birnin Kudus.

Wannan hari wanda har ila yau ya raunata wasu yahudawa da dama, shi ne mafi muni da ya auku a cikin 'yan shekarun nan a birnin.

Harin dai wata alama ce da ke kara nuna rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce Isra'ila za ta mayar da martani cikin fushi, inda ya zargi Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da ruruta wutar rikicin.

Bayanai na cewa 'yan sanda sun harbe matasan Falasadinawan biyu har lahira, wadanda kuma 'yan uwan juna ne, sai dai iyalansu sun jinjina musu kan wannan hari da suka kai

To sai dai tuni Shugaban na Falasdinawa da Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, suka yi Allah wadai da wannan hari, inda Mr Kerry ya bayyana harin a matsayin wani abu na rashin hankali.