An kama masu yi wa mata tsirara a Nairobi

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Lamarin yi wa mata tsirara a Nairobi ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta

'Yan sanda a birnin Nairobi sun kama mutane kusan 100 da ake zargi da hannu wajen yi wa mata tsirara a bainar jama'a.

Kakakin rundunar ya ce wani gungun mutane ne a yankin Kayole da ke wajen birnin, suka yi wa wata mata tsirara saboda shigar da suka ce ta yi na nuna tsiraici.

Hakazalika suka yi mata dukan kawo wuka a wata tashar mota a ranar Litinin da daddare.

Lamarin ya faru ne sa'oi bayan wasu daruruwan mata sun yi zanga-zangar nuna kin amincewa da irin hakan da aka yi wa wasu mata uku daban.