An kai hari a barikin jandarma a Nijar

Mahamadou Issoufou, Shugaban Nijar
Image caption Mahamadou Issoufou, Shugaban Nijar

Rahotanni daga yankin Wallam a jahar Tillabery ta Jamhuriyar Nijar na cewa wasu mutane dauke da makamai da ba a san ko su wane ne ba,sun kai hari a garin Bani-bangaize dake kusa da kan iyaka dak asar Mali.

Maharan sun kai harin ne a barikin jandarmeri na garin.

Hukumomin jahar ta Tillabery dai da hedikwatar rundunonin sojan kasar ta Nijar duk sun tabbatar da aukuwar harin sai dai ba su yi wani karin haske ba dangane da barnar da ya yi ba.

A karshen watan oktoban da ya gabata ma dai wasu 'yan kungiyar MUJAO ta kasar Mali sun kai hare hare 3 a lokaci guda a garin Zarum Darey da Mangaize,da gidan kason Wallam, hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro 9.