Majalisar dattawa ta Najeriya ta dage zaman tsawaita dokar ta baci

Harabar majalisar dokoki ta Tarayya a Abuja Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Harabar majalisar dokoki ta Tarayya a Abuja

Majalisar dattawa ta Najeriya ta dage zaman la'akari da wasikar Shugaban Goodluck Jonathan mai neman tsawaita dokar ta baci a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

Rahotanni na nuna cewar jim kadan bayan da aka gabatar da kudurin a gaban majalisar , yanayinta ya sauya a tsakankanin wasu mambobinta.

Wasu yan majalisar dattawan dai suna adawa da tsawaitawar dokar ta baci a yankin.Rahotanni sun nuna cewar bayyana rashin amincewar yan majalisa da yawa ya kawo cikas ga shiga tsakanin gaggawar da Shugaban majalisar Saneta David Mark yayi domin tabbatar da cewar an amince da wasikar .

A daidai wannan lokacin ne shugaban masu rinjaye na majalisar ya nemi yin amfani da doka ta 40 ta majalisar ya nemi da a rufe majalisar , abinda ya sa baki suka san inda dare yayi masu.