'Ku buge 'yan adawa' in ji Gwamna Shema

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamna Shema ya ce ba za su sassautawa 'yan hamayya ba

A Nigeria, gwamnan jihar Katsina, Barister Ibrahim Shehu Shema, ya bukaci 'yan jam'iyyar PDP su buge duk wani dan adawa da ya tsaya a hanyarsu.

Gwamnan ya kuma kwatanta 'yan adawa a matsayin "kyankyasai", wadanda magoya bayansa suka ce babu abin da ya cancanta da su illa kisa.

Ya ce, "Siyasar da muka yi a da, a yi wa mutanen PDP rashin kunya, a yi musu wulakanci, a ci musu fuska, mu ce a yi hakuri, to yanzu duk wanda duk ya ja ku, ku mai da masa; in ji ni. Babu sassauci".

Gwamna Shema ya ci gaba da cewa: "kuma kar ku damu da kyankyasan siyasa. Kyankyaso ko a gida a masai ake samunsa", yana mai tambayar magoya bayansa cewa "idan ka ga kyankyaso a gidanka mai kake masa".

Magoya bayan nasa dai sun ce "kashe shi ake yi", inda gwamnan ya ce "to ku buge su".

Wadannan kalamai dai sun harzuka 'yan hamayya, kuma sun bayyana su a matsayin yunkurin tayar da tarzoma.

Sun kara da cewa bai kamata mutum mai matsayi irin na gwamna ya yi su ba.

Karin bayani