Kisan ta'addanci ya karu da kashi 61

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na kan gaba cikin kungoyoyin da ke kai hare-hare a duniya

Wani bincike da aka gudanar kan ayyukan ta'addanci a duniya ya bayyana cewa adadin mutanen da 'yan ta'adda suka kashe ya karu da kashi sittin da daya cikin dari a bara.

Binciken, wanda cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya ta duniya ta wallafa, ya ce kusan mutane 18,000 ne suka mutu a hare-hare dubu goma da aka kai.

Binciken ya dora alhakin kashi biyu cikin uku na kashe kashen a kan kungiyoyi hudu: Kungiyar IS da Boko Haram da Al-Qa'ida da Taliban.

An aiwatar da yawancin kashe kashen ne a kasashe biyar, watau Afghanistan da Pakistan da Nigeria da Syria, kuma Iraqi ita ce kasar da lamarin ya fi kamari.

Binciken ya nuna cewa ayyukan ta'addanci na faruwa ne sakamakon tunzurawar da gwamnatoci ke yi wa 'yan ta'adda, da kuma laifin da suke ganin ana yi musu ba domin talauci ba.

Karin bayani