An nada Isaac Zida Firayi Minista

Lt Col Isaac Zida Hakkin mallakar hoto
Image caption Lt Col Isaac Zida

An bayyana sunan jami'in sojin da ya kwace mulki a Burkina Faso a watan jiya bayan jama'a sun yi ta zanga zanga akan titunan kasar a matsayin Firayi ministan kasar.

Shugaban wucin gadi na kasar Michel Kafando, wanda aka rantsar ranar talata ne ya nada Laftanar Kanar Isaac Zida.

Sojojin kasar ta Burkina Faso sun amince su maida mulki ga farar hulla ne bayan sun fuskanci matsin lamba daga kasashen waje. Sun dai kwace mulkin ne bayan wata zanga zanga da ta samu gagarumin goyan baya, abun da kuma ya tursasawa tsohon shugaba Blaise Campaore yin murabus.

Masu aiko da rahotanni sunce ana yabawa sojojin kasar saboda hana kasar afkawa cikin rudani, amma sun kara da cewa ana daukar Laftanar kanar Zida a matsayin daya daga cikin tsaffin hannu na gwamnatin da ta sha shude.