An kama jagoran addinin Hindu a India

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Shugabannin addinin ya dade yana yi wa 'yan sanda layar zana

'Yan sanda a jihar Haryana da ke arewacin India sun cafke jagoran addinin Hindu, wanda magoya bayansa suka kwashe kwanaki biyu suna dauki-ba-dadi da su.

Mutane akalla mutum shida suka mutu, yayin da daruruwan jama'a suka jikkata a lokacin gumurzun.

'Yan sandan dai na tuhumar malamin addinin, mai suna Rampal Maharaj da aikata laufuka da dama, ciki har da yin fito-na-fito gwamnatin Indiyar.

Jagoran addinin dai ya sha zille wa 'yan sanda a kokarin da suke yi na kama shi a baya.