INEC na shan korafi kan katin Zabe

Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega
Image caption Ana ta korafi game da tsaikon da aka samu na bada katin katin zabe na din-din-din.

Hadaddiyar kungiyar fafatikar kare hakkin bil'adama ta CODER ta ce idan ba ayi a hankali ba, da wuya a iya gudanar da zaben da zai zama karbabbe ga al'ummar Nigeria a shekarar 2015.

Kungiyar ta ce matakan da hukumar zabe ta fara dauka na killace masu kada kuri'a da kuma amfani da wata manhajar na'ura wata hanya ce da zata haifar da magudi.

CODER ta zargi hukumar zaben kasar da cewar jihohin da ke adawa da gwamnati mai mulki irin Kano da Lagos da Rivers aka rage yawan mutanen da za su samu katin zabe na din-din-din.

Domin gwamnan jihar Lagos Babatunde Fashola ya je mazabarsa don karbar katin zabe da ya yi rijista amma bai samu ba.

Sai dai hukumar ta ce babu wani da za'a killace daga samun katin zabe na din-din-din.