An kara kai samame a Masallaci a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun ce sun gano makamai a masallacin

'Yan sanda a kasar Kenya sun sake kai wani samame a wani masallaci da ke garin Mombasa.

Wannan shi ne samame na uku cikin mako guda da 'yan sandar ke kai wa.

A cewar 'yan sandan, sun samu makamai da gunrneti-gurneti da kuma bam din da ake hadawa da man fetir.

Shugaban rundunar 'yan sandan ta Mombasa Richard Ngatia, ya ce matasa masu tsatsauran ra'ayin ne suka mamaye masallacin yayin da shi kuma ministan cikin gida a kasar ta Kenya Joseph Ole Lenku ke cewa za a ci gaba da kai samamen har sai cikakken tsaro ya samu a garin.

Sai dai manyan malaman yankin sun yi gargadi ga jami'an tsaro da su guji tunzura matasan domin kaucewa irin wannan lamari da ke faruwa.