Ana zaman dar-dar a jihar Nasarawa

Gwamna Al Makura Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Gwamnan jihar Nasarawa

A Najeriya ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Nasarawa da ke arewacin kasar bayan wasu tashe-tashen hankula a jihar.

Al'amarin ya haddasa asarar rayuka da kuma kone konen gidaje jiya a wasu yankuna da ke kusa da lafia babban birnin jihar.

Rundunar 'yan sanda ta jihar ta tabatar da barkewar rikicin na jiya amma ta ce ta baza jami'anta zuwa wadannan yankuna domin kwantar da tarzomar.

Sai dai har yanzu harkokin gwamnati da suka hada da makarantu da kuma bankuna na cigaba da kasancewa a rufe, kuma har yanzu dokar hana zirga zirgar da aka sanya tana aiki.