Ta'addanci: Nigeria ce ta hudu a duniya

Image caption Hare-haren Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria

Wani bincike kan ayyukan ta'addanci a duniya ya nuna cewa Nigeria ta hudu wajen aikata kisan ta'addanci a duniya.

Binciken, wanda cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya ta duniya ta wallafa, ya ce an kashe mutane 1,826 a hare-hare 303 da aka kai a shekarar da ta wuce a kasar.

Rahoton ya bayyana cewar kasar Iraki ce ta farko a duniya wajen aikata ayyukan ta'addanci a duniya inda a shekara ta 2013 aka kashe mutane 6,362 a hare-hare 2,492 da aka kai.

A jumlace a cewar rahoton kusan mutane 18,000 ne suka mutu a hare-hare 10,000 da aka kai.

Binciken ya dora alhakin kashi biyu cikin uku na kashe kashen a kan kungiyoyi hudu: Kungiyar IS da Boko Haram da Al-Qa'ida da kuma Taliban.

Kasashe biyar da ke kan gaba a kisan ta'addanci:

  • Iraki - harin sau 2,492 a shekarar 2013, mutane 6,362 sun mutu.
  • Afghanistan - hari sau 1,148 mutane 3,111 sun mutu.
  • Pakistan - hari sau 1,933 mutane 2,345 sun mutu.
  • Nigeria - hari sau 303 mutane 1,826 sun mutu.
  • Syria - hari sau 217 mutane 1,078 sun mutu.
Hakkin mallakar hoto BBC World Service