An koma hayar Achaba a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption Gwamnatin jihar Kaduna ta tanadi taar ko zaman wakafi ga wanda ya karya wanann doka.

A kwanakin baya ne gwamnatin jahar Kaduna ta Nigeria ta kafa dokar hana hayar Babura ko kuma Achaba da kuma hana goyo a Babura domin abinda gwamnatin ta ce hana hare-hare da akan kai da Babura.

Yawancin hare-haren da akan kai ta hanyar jefa ababen fashewa ana kai su ne akan Babura, wanann dalili ne ya sa ko a wajen binciken ababen hawa na jami'an tsaro ba a yadda mutum ya wuce akan Babur ba sai dai ya sauka ya tura.

To amma 'yan watanni bayan kafa wannan doka wacce ta tanadi tara ko dauri ga duk wanda ya karya ta, wasu a jahar sun dawo da yin hayar Babura da kuma daukar fasinjoji.

Yawancin wadanda wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewar rashin aikin yi ne ya sa suka koma tsohuwar sana'ar ta su, duk kuwa da cewar sun san idan hukuma ta kama su za su fuskanci tara.

Kafin jihar Kaduna ta kafa wannan doka, jihar kano ce ta fara kakaba wannan doka ta hana yin hayar babur ko goyo.

To sai dai daga baya gwamnatin jihar ta yi sassauci ga magidancin da ya goyo iyalinsa ko yaransa, wanda daag bisani ta janye ganin wasu masu karya doka sun fara yin karya da hakan.