Ana bukin ranar makewayi ta duniya

Wani makewayi na jama'a a Afurka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashe da dama na fuskantar karancin makewayi.

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar makewayi ta duniya.

Wannan rana ta zo a yayin da al'ummomin wasu kasashe da birane kimanin biliyan daya - ke yin ba haya a bainar jama'a.

Kasashe irinsu India na daga cikin wadanda suke da karancin makewayi, hasali ma hakan na da nasaba da yawan yi wa mata fyade a lokutan da suka fito kewayawa da daddare saboda nisan da ke tsakanin gidajensu da bandakunan.

Babbar barazanar a yanzu itace yadda cutar Ebola ta fara rarakar wasu kasashen Africa, da kuma daya daga alamun hanyoyin kamuwa da cutar ita ce yawan cudanya ko hada makewayi da mutane barkatai.

A jihar Lagos da ke kudancin Nigeria ma mutane sun koka da karancin bandakunan da jama'a ke amfani da su wala a kasuwanni ko a tituna idan bukatar kewayawa ta kama su.

Wannan dalili ya sa wasu kan tsuguna a duk inda suka samu domin sauke nauyi.