Boko Haram sun kashe mutane 45

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban 'yan bangar garin ya ce 'yan Boko Haram sun je ne a cikin motoci dauke da muggan makamai.

A Nigeria, ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kisan mutane 45 a wani hari da suka kai kauyen Kuyen Azaya Kura da ke cikin jihar Borno.

Shugaban 'yan banga na garin, Muhammed Gava ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AP cewa 'yan Boko Haram sun je garin ne ranar Laraba a cikin motoci dauke da muggan makamai.

Wani rahoto ya ce sauran mutanen kauyen da suka tsere sun fantsama cikin daji suna neman mafaka.

Shugaban karamar hukumar Mafa na riko, Shettima Lawan ya bayyana harin a matsayin wani abu na mugunta kuma abin kunya.

Karin bayani