Sabon Layin dogo daga Lagos zuwa Calabar

Jiragen kasa a Nigeria
Image caption Jiragen kasa a Nigeria

Wani kamfanin kasar China ya sanya hannu a kan wata kwangila ta dola biliyan 12 domin gina layin dogo a gefen gabar tekun Nigeria

Kamfanin ya bayyana wannan kwangila da cewar ita ce kwangila daya tilo mafi girma da China ta kulla da wata kasar waje.

A jiya laraba ne kamfanin jiragen kasa na kasar China, CRCC ya rattaba hannu akan yarjejjeniyar tare da gwamnatin Nigeria a Abuja.

A karkashin kwangilar za a gina layin dogo mai nisa kilomita 1,402 a gefen gabar tekun Nigeria, inda za a hada babban birnin kasuwanci na Lagos da birnin Calabar na jihar Cross River.

Kwangilar ta dola biliyan 11.97 ita ce kwangila mafi tsoka da China ta kulla da wata kasar waje.

Duk da karfin tattalin arzikin Nigeria, kasar na fama da matsalolin hanyoyin sufuri ta jiragen kasa.

Ana sa ran wannan kwangila zata samar da aikin yi ga mutane 200,000

A bara dai cinikayya tsakanin Nigeria da China ta kai dola biliyan 13.6