Najeriya: 'Yan majalisa sun kira Sufeto Janar

sufeto janar Hakkin mallakar hoto Nigeria Police

‘Yan majalisar wakilai a Najeriya sun nemi Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da ya gurfana a gabansu don ba da bahasi a kan yunkurin da ‘yan sandan suka yi na hana su zaman majalisar.

Sun ce ya gurfana ne a gabanta gobe Jumma’a.

Hakan ya biyo bayan watsa hayaki mai sa hawaye ne da 'yan sandan Najeriyar suka yi a yunkurin hana majalisar zama.

Ko da yake a nasu bangaren, ‘yan sandan sun fitar da sanarwa a kan dalilan da suka sa jami'ansu suka fesa borkonon tsohuwa a kan 'yan majalisar ciki har da kakakin majalisar wakilan, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

A wata rubutacciyar sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce sun dauki wannan mataki ne bayan da suka samu wasu bayanan sirri da ke cewa 'yan bangar siyasa za su yi kokarin kutsa kai cikin zauren majalisar.

Wannan lamari dai ya sa an dage zaman da majalisar ta shirya yi don muhawara game da batun wa'adin dokar-ta-baci a wasu jihohi uku dake arewa maso gabashin kasar da ke fama da rikicin Boko Haram

'Yan Majalisar dai sun zargi 'yan sanda ne da hana Kakakin majalisar shiga majalisar, shi da sauran 'yan majalisu na bangaren 'yan adawa.

Lamarin dai ya haifar da rikici.

A kwanan baya ne dai kakakin majalisar ya koma jam'iyar adawa ta APC.