'Mun yi kokarin tabbatar da doka ne a majalisa'

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Sufeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Sulaiman Abba

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce ta tura jami'anta zuwa majalisar dokokin kasar ne saboda kokarin tabbatar da doka da oda.

Sanarwar da 'yan sandan suka fitar ta ce sun samu bayanan sirri ne cewa wasu bata-gari da 'yan banga za su yi kutse a majalisar dokokin kasar shi ya sa suka tura jami'ansu domin tabbatar da cewa lamarin bai wuce guna da iri ba.

'Yan sandan sun ce sun soma tantance 'yan majalisa ne, sai Alhaji Aminu Tambuwal tare da dandanzon magoya bayansa suka lalata shinge da 'yan sanda suka yi sannan suka ci zarafin 'yan sandan.

Sanarwar ta gargadi 'yan siyasa su mutunta dokokin kasar kuma su daina amfani da 'yan banga domin cimma burinsu.

A yanzu haka shugaban majalisar dattijai, David Mark, ya ba da umurnin rufe majalisar dokokin har sai makon mai zuwa.