Sojoji sun kwato garuruwa 3 a Adamawa

Sojojin Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Nigeria

Rundunar sojojin Nigeria ta ce sojojinta sun kwato garuruwa guda 3 a Jihar Adamawa daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

A cikin wani sako da ta aika ta twitter a jiya, hedkwatar tsaron Nigeria ta ce a yanzu sojojinta suna da cikakken iko da garuruwan Gombi da Pelia da kuma Hong.

Haka nan kuma rundunar ta ce ta kama wasu daga cikin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kuma makamai.

Rundunar sojojin ta ce ta fara wani yunkuri na sake kwato dukkanin garuruwan da yan kungiyar Boko Haram suka kwace.

Wata sanarwa ta ce dama a karshen mako sojojin sun fatattaki 'yan kungiyar Boko Haram daga garin Chibok bayan da ya shafe kwanaki biyu a karkashin ikonsu.

A cikin 'yan watannin nan kungiyar Boko Haram ta zafafa kai hare hare inda ta kame garuruwa da dama da suka hada da Mubi, gari na biyu mafi girma a jihar Adamawa.

Har yanzu dai akwai rashin tabbas akan yanayin da garin na Mubi ya ke ciki. Yayin da hukumomi suka an kwato shi ta hanyar amfani da marhaba, wasu mazauna garin da suka fice zuwa Yola sun ce har yanzu 'yan kungiyar Boko Haram na sintiri a cikin garin na Mubi.