An harbawa Tambuwal bakonon tsohuwa

Majalisar wakilan Nigeria Hakkin mallakar hoto peoples daily
Image caption Majalisar wakilan Nigeria

Kakakin majalisar wakilan Nigeria ya kutsa kai da karfin tuwa zuwa cikin harabar majalisar.

Tun farko dai 'yan sanda sun hana kakakin shiga harabar Majalisar.

Haniya ta barke, inda 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa.

Wakilin BBC ya ce da karfi 'yan majalisar suka bankare kofar majalisar domin bayar da dama ga kakakin ya shiga cikin majalisar

Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya isa kofar majalisar ne tare da tawagarsa inda yan sanda da ke bakin kofar suka hana shi shiga.

Tambuwal ya shaidawa 'yan sandan da ke bakin kofa cewa shine kakakin majalisar, amma duk da haka

Kakakin majalisar ya umarci dukkanin 'yan majalisar su dawo daga hutu a yau domin tattaunawa akan bukatar tsawaita dokar ta baci da shugaban kasa ya gabatar.